'Hamas za ta tsagaita bude wuta'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A kusa da garin Halhul aka gano gawarwakin wasu matasa Yahuwa da aka kashe

Rahotanni daga Gaza sun ce kungiyar Falasdinawa ta Hamas ta ce a shirye take ta dakatar da kai hare-hare da makaman roka a kan garuruwa da biranen Isra'ila, in har Isra'ilar za ta daina kai hare-hare a kan zirin.

Jami'an gwamnatin Masar ne suka shiga tsakani aka fara ganin alamun cimma wannan tsagaita bude wutar.

Wakilin BBC a birnin Kudus ya ce mai yiwuwa wannan yunkuri ya kwantar da hankula a Gabashin Birnin Kudus yayin da ake shirye-shiryen jana'izar Mohammed Abu Khdair, wani matashi Bafalasdine da aka kashe a farkon mako.

Kisan matashin ya biyo bayan kisan wadansu matasa ne su uku 'yan Isra'ila.

Karin bayani