Sojoji sun kona manyan motoci a Legas

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An jima ana zargin sojin Najeriya da wuce makadi da rawa

Rahotanni daga Lagos a Nigeria na cewa sojoji sun killace wasu tituna inda suka rika harba bindiga sama tare da kona manyan motocin bas-bas.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce hakan na da nasaba da kashe wani soja a wani hatsarin bas da ya faru a babbar hanyar Ikorudu.

Sojojin dai sun kona manyan Bas guda hudu, haka kuma sun lalata wasu motocin hudu.

Gwamnatin jahar ta Legas ta kaddamar da bincike game da lamarin.