'Mun kama mata 'yan Boko Haram'

'Yan Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane da dama sun hallaka a hare hare Boko Haram a Nigeria

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kama wasu mata uku da take zargi da yiwa kungiyar Boko Haram leken asiri da kuma horar da mata 'yan uwansu domin shiga cikin kungiyar.

Wata sanarwa da kakakin shalkwatar tsaron Najeriya Manjo Janar Chris Olukolade ya aike wa BBC, ta ce sun gano matan ne, bayan wani yunkuri da wata mace ta yi na kai harin kunar bakin wake a kan sojoji a jihar Gombe.

Sanarwar ta kara da cewa, wata mata mai suna Hafsat Bako, wacce sojojin suka fara kamawa a farkon wannan makon, ita ce jagorar sauran matan da suka hada da Zainab Idris da kuma Aisha Abubakar.

Sojojin sun ce sun kama matan ne a kan hanyarsu ta zuwa garin Madagali na jihar Adamawa, inda daga bisani suke sa ran karasawa cikin daji domin haduwa da sauran 'yan kungiyar ta Boko Haram.

Babu dai wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin da sojoji suka yi na cewa matan 'yan kungiyar Boko Haram ne.