Mubarak Bala ya bar asibiti a Kano

Mubarak Bala
Image caption Mubarak Bala ya rika yada halin da ya ke ciki ta shafinsa na twitter

Matashi dan Nigeria Mubarak Bala da a kwanakin baya ya ce bai yi imani da Allah ba, ya ce ya janye wasu kalaman batanci da ya yi.

Wata sanarwa da ta fito daga hannu lauyan da ke kare matashin ta ce, tuni Mubarak Bala ya sasanta da 'yan uwansa ba tare da wani ya tilasta masa ba sakamakon matsalar data taso bayan kalaman da ya yi.

Sanarwar ta kara da cewa, matashin ya ce ya janye daukar duk wani mataki na neman taimako daga wasu wurare kamar yadda ya ce zai nema tun da farko.

Shi dai Mubarak Bala mai shekaru 29 an tsare shi ne a asibitin masu tabin hankali da ke Kano, bayan danginsa wadanda Musulmi ne sun nemi a bincika ko wani abu ne ya taba lafiyarsa bayan furucin da ya yi.

Wannan al'amari dai ya ja hankalin wata kungiya mai da'awar kare hakkin wadanda ba su da addini mai suna International Humanist and Ethical Union, wadda ta shiga kiran a sake shi.