Google ya dawo da wasu shafuka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Google na daya daga cikin manyan hanyoyin samun bayanai ta intanet

Google ya mika kai ga matsin lambr da ake masa na dawo da wasu hanyoyin shiga wasu shfuka da ya cire daga rumbunsa.

A farkon watan nan na Yuli, Google ya cire wasu kasidu da jaridar Guardian ta sanya a intanet, amma yanzu ya dawo da su gaba daya.

Kamfanin yana kokarin bin ka'idar dokokin Kotun Turai ne (ECJ) kamar yadda ya ce, na fitar da hanyoyin samun shafukan da ake ganin sun tsufa ko ba su da amfani ko kuma muhimmancinsu ya kare.

Kafar ta Google ta ce hukuncin sa ta ta dawo da hanyoyin kai wa ga shafukan da fitar da kotun Turai ta yi, ba abu ne da suke maraba da shi ba, ko suke so, illa dai saboda doka ce kuma za su kiyaye da ita.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Google ya kare matakin nasa na cire hanyoyin samun shafukan da ake ganin ba su da muhimmancin da cewa , ba abu ne mai sauki ba.

Hukuncin kotun ya biyo bayn matakin da editan BBC na fannin tattalin arziki Robert Peston, ya dauka ne bayan an ankarar da shi cewa za a daina ganin wasu kasidu da ya sa a intanet, wadanda ya rubuta a 2007, daga Google.

Bayan kasidun na Peston, wasu na BBC guda bakwai ma kafin hukuncin an shirya fitar da su.

Bayan hukuncin na sanya Google dawo wa da shafukan da ya fitar, editan BBC na ayyuka na musamman, James Ball ya rubuta cewa wasu kasidun BBC shida da ya ce matkin ya shafa, ''an manta da su'' sun dawo.