An kama wasu Yahudawa akan kisan Khdeir

Hakkin mallakar hoto Reuters

Hukumomin Isra'ila sun kama wasu Yahudawa bisa zargin hannu a kisan da aka yi cikin makon jiya na saurayin nan Bapalasdine, Muhammad Abu Khdeir.

An sace matashin ne ranar Laraba da safe goshin asubahi, a wani titi kusa da gidansu, daga bisani aka tsinci gawarsa a daji.

Kafafen yada labarai sun ambaci wani jami'i da ba a bayyana sunansa ba yana cewa 'yan sanda na zargin kisan na da nasaba da dalilai na nuna kishin Yahudanci.

Kisan dai ya janyo mummunar tarzomar Palasdinawa , bayan da aka fara rade radin cewa kisan ramuwar gayya ne da wasu Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi suka aikata kan kisan wasu matasan Yahudawa uku a watan jiya.

Isra'ila dai ta dora alhakin kisan su kan kungiyar kishin Palasdinawa ta Hamas, zargin da ita kuma ta musanta.

Karin bayani