An kashe mutane da dama a Uganda

Jami'an tsaron kasar Uganda sun ce an kashe mutane da dama a wasu hare hare da wasu dauke da makamai suka kai a yammacin kasar.

'Yan sanda akalla uku ne aka kashe lokacin farmaki kan wasu sansanin 'yan sanda da na soja.

Rahotanni na cewa jami'an tsaron Uganda sun kashe wasu daga cikin maharan, akwai rahoton dake cewa wadanda aka kashen zasu haura arba'in.

Har yanzu babu tabbas kan wadanda suka kai hare haren a gundumomin Bundibugyo da Kasese, da ke kan iyaka da jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Wasu rahotanni na cewa rikicin na kabilanci ne, wasu kuma na cewa wata kungiyar 'yan kishin Islama ce ta kai hare haren.