Amurka ta bukaci karin bincike a filayen jirage

Jami'an tsaro a filin jirgi Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Jami'an tsaro a filin jirgi

Jami'an tsaron Amurka sun bada karin haske kan wasu sabin matakai da suke son aiwatarwa a wasu filayen jiragen sama na kasashen waje, inda jirage kan tashi kai tsaye zuwa Amurka.

Hukumar tsaron da ya shafi ayyukan sufuri ta ce akwai yuwuwar jami'an tsaro a filin jirgi su bukaci pasinjoji dake dauke da wasu na'urori na latironi, ciki har da kwamputoci, da wayoyin salula, da su kunna su, domin tabbatar da cewar akwai batur a jikinsu.

Ranar Laraba ne Amurkar ta bada sanarwar tsaurara matakai, bayan damuwar da aka shiga cewa wasu mayaka 'yan gwagwarmayar Islama na hada wasu irin nakiyoyi da jami'an tsaro ba za su iya gano ba a filin jirgin sama.