Sabuwar dokar kunna na'ura a filin jirgin sama

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Amurka ta nemi a tsaurara matakan tsaro a wasu filayen jiragen sama na kasashen waje

Filayen jiragen sama na Heathrow da Manchester sun fadawa fasinjoji cewa su tabbatar dukkanin na'urorinsu na Lataroni suna da caji idan har zasu tashi ne zuwa Amurka

Wannan mataki ya biyo bayan wata bukatar Amurka na neman wasu filayen jiragen sama na kasashen ketare su tsaurara matakan tsaron su

Wata sabuwar doka ta tanadi cewa 'idan har kana da na'ura kuma bata kunnu ba, to ba za a bari ka shiga da ita cikin jirgi ba'.

Sai dai za a aiwatar da wannan dokar ta hanyoyi daban daban a filayen jiragen saman guda biyu

Za a caje na'urar fasinja a filin jirgin sama na Heathrow a wurare biyu da suka hada da kofar da zaka karbi tikitin shiga jirgi.

A filin jirgin sama na Manchester kuwa, wata mai magana da yawun filin jirgin ta ce jami'in kamfanin jirgin ne zai caje na'urar da Fasinja yake dauke da ita a kofar da fasinjoji ke jira kafin su tashi

Kamfanin jirgin sama na British Airways ya ce za'a bukaci kwastomomin da aka gano cewa na'urorinsu ba su da caji, su sake tsaida wata ranar da zasu tashi

British Airways ya kara da cewa duk fasinjan da ya sayi sabuwar waya a kantin filin jirgi, dole ne ya tabbatar da cewa tana da cajin da za'a iya kunna ta

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dole ne wayoyi su kasance suna da caji kafin a shiga da su cikin jirgi a Heathrow da Manchester

Ma'aikatar sufuri taki cewa ko sauran filayen jiragen saman Birtaniya zasu tilasta amfani da wannan doka a jiragen da suke tashi zuwa Amurka

Filin jirgin sama na Heathrow ya sanarwa da fasinjojin sa wadannan sabbin dokoki ta hanyar shafukan sa na Facebook da kuma na yanar gizo

Masu sharhi sun nuna cewa wannan mataki ya biyo bayan wani yunkuri da mayakan Islama a Syria da Yemen suke yi na kirkirar wani bam da zai iya kaucewa jami'an tsaro.

Kamfanonin jiragen sama na Virgin Atlantic da Delta Air Lines da kuma Air France basu bada cikakken bayanai ba game da yadda zasu tunkari irin wannan yanayi a lokacin da BBC ta nemi jin ta bakin su.