Tsohon Shugaban Georgia ya rasu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Margayi Shugaba, Eduard Shevardnadze

Tsohon Shugaban kasar Georgia, Eduard Shevardnadze ya rasu yana da shekaru tamanin da shida a duniya.

Shi ne ministan harkokin kasashen waje a tarayyar Soviet na karshe kafin rugucewar kasar kuma ya jagoranci hudda da yammacin duniya a karkashin shugaba Gorbachev.

Daga nan sai Shevardnadze ya koma Georgia inda a matsayinsa na Shugaban kasa ya kawo daidaito a wani lokaci na rashin tabbas.

A shekara ta 2003 ne masu zanga-zanga suka kifar da gwamnatinsa sakamakon wani gangami na bore da aka yi wa lakabi da "Rose Revolution".