Ana neman gawar Castro na Ghana

Hakkin mallakar hoto Castrounderfireinstagram
Image caption Castro ya tafi gabar teku a Ghana

'Yan sanda a Ghana suna kokarin gano gawar wani shahararren mawakin kasar mai suna Castro wanda ya gamu da hadari a cikin jirgin ruwa.

Rahotanni sun nuna cewar hadarin ya afku lokacin yana tare da wata mata a cikin jirgin ruwa.

Manajansa, DJ Amess ya ce Castro ya dawo Ghana ne a ranar Alhamis kuma yana shakatawa ne tare da abokansa ciki hadda dan kwallon Black Stars, Asamoah Gyan.

Abokan Castro sun soma mika ta'aziyarsu, duk da cewar ba a bayyana a hukumance ba ko rasu ko yana da rai.

Castro wanda sunansa na asali Theophilus Tagoe, yana da farin jini a Ghana.