Isra'ila da Hamas na musayar wuta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An jikkata Falasdinawa akalla 14 ya zuwa yanzu

Israila tace ta kaddamar da wasu hare hare ta sama a wurare hamsin a zirin Gaza a cikin dare, kuma rahotanni na baya bayannan na cewa an jikkata akalla Palasdinawa 14.

Dakarun Kasar sunce an kaddamar da farmakin ne da nufin dakatar da makaman rokar da ake harbowa daga Yankin

An dai harba makaman roka kusan casa'in a ranar Litinin kadai.

Wakilin BBC a Gaza yace Faslsdinawan sun mayar da martani ta hanyar harba makamakin Roka, kuma Israilan ta bukaci 'yan kasar ta dake kudancin Kasar dasu zauna a yankunan da suke da kariya.

Zaman dar dar ya karu ne tun lokacin da aka kashe wani matashi bafalasdine, tare kuma da sacewa da kuma kisan wasu matasan Isra'ila su uku kafin sannan.