An kashe akalla mutum guda a Kaduna

Hakkin mallakar hoto KDGH
Image caption An ce jami'an tsaron na Nigeria sun tafi da mai gidan da abin ya faru.

Rahotanni daga birnin Kaduna na arewacin Nigeria sun ce akalla mutum guda ya rasa ransa a wata musayar wuta da aka yi tsakanin jami'an tsaro da mazauna wani gida da ake zargin 'yan Boko Haram ne.

Mazauna unguwar Kinkinau sun bayar da labarin cewa an dauki lokaci mai tsawo ana musayar wutar.

An ce jami'an tsaron sun je unguwar ne bayan da aka tsegunta musu cewa akwai wani babban shugaban kungiyar nan ta Boko Haram a unguwar, kuma sun fuskanci turjiya ne lokacin da suka yi yunkurin shiga gida.

Har yanzu dai jami'an tsaron Nigeria ba su yi wani bayani ba dangane da faruwar al'amarin.

Karin bayani