Sabon rikici ya barke a Afrika ta Tsakiya

Sabon rikici a Jumhuriyar tsakiyar Afrika
Image caption Sabon rikici a Jumhuriyar tsakiyar Afrika

Wani sabon rikici ya barke a birnin Bambari na Jamhuriyar tsakiyar Afrika tsakanin kiristoci da kuma musulmai a yankin.

Rahotanni sun ce tashin hankalin tamkar ramuwar gayya ce da musulmai suka kai a kan kiristoci bayan tashin wani bam a cikin masallacin Paoua mai iyaka da kasar Chadi.

Hakan na faruwa ne yayinda Ministan tsaro na Faransa Jean Yves le Drian ke fara wata ziyara a yankin.

A kwanakin baya Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya, Ban Ki-moon ya ce ana bukatar karin 'yan sanda da sojoji 3,000 a jamhuriyar dimokradiyyar Congo domin kare fararen hula daga rikicin da ake fama da shi.

Karin bayani