Binciken masana kan gigin tsufa

Hakkin mallakar hoto SPL

Masana kimiyya sun yi wani babban hobbasa wajen gano somin cutar gigin tsufa ta hanyar gwajin jinin mutum

Binciken da aka gudanar a cikin mutane fiye da 1,000 ya gano wasu furotin dake cikin jini da ka iya hasashen lokacin da cutar gigin tsufa take kama mutum tare da bada tabbaci na kashi 87 cikin 100

Binciken wanda mujallar Alzheimer's & Dementia ta wallafa, za a yi amfani da shi wajen inganta gwaje gwaje ga sabbin magungunan cutar gigin tsufa

Bincike game da maganin cutar da ya gamu da cikas. Tsakanin shekarar 2002 da kuma 2012, kashi 99.6 cikin 100 na gwaje gwaje da aka yi da nufin kare kamuwa da cutar bai yi nasara ba

Alamun cutar dai sun hada da mantuwa da kuma rikicewa- manta sunayen mutane ko kuma yadda zaka je gida

Hakkin mallakar hoto Jeff Overs BBC

Daga bisani kuma mutane sai su soma fuskantar wahalhalu a wasu hidimomi da suke yi kamar zuwa saayayya da yin girki Alamomin cutar dai suna kara dagulewa ne a cikin sannu sannu kuma ba'a warkar da cutar sai dai a bada magani da ka iya rage wa mutane karfin cutar

Kusan mutane 750,000 a Birtaniya suna da cutar gigin tsufa Cutar na iya shafar manya da suka hada da mata da maza. Amma ana iya samun ta cikin mutane masu karancin shekaru

Kusan kashi biyu bisa uku na mutanen dake fama da cutar dai mata ne, saboda kasancewar sun fi maza tsawon rai

Idan mutum na fama da cutar, ba ya nufin cewa a garzaya da shi gidan kula da gajiyayyu ko kuma asibiti.

Kashi biyu bisa uku na mutanen da ke dauke da cutar na rayuwar s a cikin al'umma

Haka kuma tsufa tukuf ba shine yake nufin zaka kamu da cutar gigin tsufa ba. Kawai dai an fi samun ta ne a cikin manya.