'Yan Isis sun kwace Sinadaran Nukiliya

'Yan kungiyar Isis Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun Isis sun samu gagarumar nasara ta hanyar amfani karfin bindiga

Iraki ta gargadi Majalisar Dinkin duniya cewa 'yan tada-kayar-bayan sunni sun kwace kayayyakin sarrafa Nukiliya da masana kimiyya ke amfani da su a wata jami'a da ke birnin Mosul.

Wata wasika da jakadan kasar ya aika wa majalisar dinkin duniya ta bukaci taimakon kasashen duniya ta re da gargadin cewa, kayayyakin ka iya bai wa mayakan Isis damar kaddamar da hare-haren ta'addanci.

Hukumar kula da makamashin Nukiliya ta duniya ta ce ta yi imanin cewa kayayyakin da 'yan Isis suka kwace na da raunin inganci kuma ba za su iya janyo wata babbar barazanar tsaro ba.

Tun farkon watan Yuni, kungiyar Isis wadda ta sauya suna zuwa "Gwamnatin Islama" ta fadada tungarta da ke gabashin Syria,inda ta kwace Mosul birni na biyu a Iraki, ta kuma dangana da tsaunin Euphrates tana yi wa birnin Bagadaza barazana.