Bukin samun 'yanci a Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu
Image caption Kimanin mutanen miliyan daya da rabi ne suka rasa muhallansu a Sudan ta Kudu.

A ranar Laraba ne kasar Sudan ta Kudu ke bukin cika shekaru uku da samun 'yancin kai daga Jamhuriyar Sudan.

A baya dai mutane da dama na ganin samun 'yancin kai ka iya kawo karshen tashe- tashen hankula da aka kwashe shekaru ana fama da su.

Sai dai rikice -rikicen siyasa na cikin gida sun haifar da yakin basasa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban jama'a tare da raba wasu mutane miliyan daya da rabi daga muhallansu.

A yanzu dai Sudan ta Kudun na fuskantar barazanar fari da kuma barkewar cutar Kwalara.