Ana zargin kamfanonin Birtaniya da taimakawa Syria

Image caption Iskar gas ta 'Sarin' ta yi sanadiyyar kashe rayuka da dama a Syria

Ana tsammanin ofishin kula da harkokin kasashen waje na Birtaniya zai maida martani game da zarge zargen cewa kamfanonin Birtaniya sun sayarwa da Syria wasu sinadarai da aka yi amfani dasu wajen samar da iskar nan mai guba ta 'Sarin'.

BBC ta samu wata takadda da ta nuna cewa Birtaniya ita ce ta samarwa da Syrian biyu daga cikin mahimman sinadaran da akai amfani da su wajen samar da wannan gas.

An danganta amfani da iskar 'Sarin' din da mace macen daruruwan mutane a lokacin yakin basasar Syria na shekaru 3.

Jama'a da dama kuma sun tamu tawaya ta wannan hanya.