Maganin kashe kwari na kashe Tsuntsaye a Turai

Image caption Maganin kashe kwari na Imidacloprid ya bazu a kasuwa

Wani bincike da aka gudanar ya danganta yadda ake yawaita amfani da wani irin maganin kashe kwari da aka ce shine yake kashe kudan zuma da kuma raguwar da ake samu a irin tsuntsayen da ake da su a Turai

Sinadarin kashe kwarin na 'Imidacloprid', ana yawaita amfani da shi a fannin ayyukan gona domin kashe kwari.

Masana kimiyya a Dutch sun ce bayanai sun nuna cewa wannan sinadari na kashe kwarin nada alaka da kashe nau'in tsuntsun da aka sani.

Amma wadanda suke samar da sinadarin kashe kwarin sun ce babu hujjar dake tabbatar da abinda ake tunani

Sinadarin kashe kwari na 'Imidacloprid' na daya daga cikin magungunan kashe kwari da aka kirkiro a shekarun 1990 a matsayin wata hanya mai kyau ta magance kwarin da ke addabar kayan abinci da aka noma.

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Masu bincike na bukatar a gudanar da mahawara kan wannan batu

An sami nasara kwarai wajen amfani da Irin wannan maganin kashe kwari kuma a yanzu yawansa a kasuwar magungunan kashe kwari ya kai kusan kashi 40 cikin 100.

Sai dai ana kara nuna damuwa game da tasirin da irin magungunan suke yi ga muhalli.

Wasu jerin binciken da aka gudanar sun danganta su da raguwar da ake samu na kudan zuma

A yanzu dai masana kimiyya a Dutch a karon farko sun nuna alakar dake tsakanin amfani da Imidacloprid da kuma raguwar tsuntsayen da ake gani

Masu binciken dai sun bukaci a gudanar da wata mahawara ta siyasa game da amfani da irin wadannan magungunan kashe kwari