Burundi za ta rage yawan coci-coci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Majami'u na karuwa a Burundi tun bayan yakin basasa

Majalisar wakilai a kasar Burundi ta amince da kudurin da ke da aniyar rage yaduwar wuraren ibada na Kiristoci ko coci-coci.

Wani bincike da gwamnati ta gudanar bara ya gano cewa akwai majami'u 557 da ke gudanar da ayyukansu a kasar ta Burundi.

Sabuwar dokar za ta bukaci kowanne coci ya samu magoya baya akalla 500 tare da cikakken wurin zama.

Coci-cocin da ke bin darikar Evangelical sun karu sosai bayan yakin basasar da aka dade ana yi a kasar wanda ya kare a shekara ta 2005, bayan kisan mutane 300,000.

Wakilin BBC a kasar Prime Ndikumagenge, ya ce kudurin ya samu gagarimin goyon baya daga 'yan majalisar wakilan kasar, kuma ana sa ran majalisar dattawa ma ta amince da shi.