Manoma a Nigeria sun yi gargadin karancin abinci

Hakkin mallakar hoto
Image caption Manoma na gudun hijira a yankunan da ake fama da rashin tsaro

Hare haren 'yan bindiga a yankunan Jihohin Arewa maso gabashin Najeriyar dama wasu sassa a Arewacin kasar na shafar manoma matuka a yankunan.

Kungiyar Manoma ta Najeriya na nuna tsoron gudun hijirar da manoma ke yi daga kauyuka zuwa birane dama wasu Jihohi a kasar, ka iya barazana ga yawan abincin da yankin Arewacin kasar zai iya samu a daminar bana.

Mai magana da yawun Kungiyar Manoman Alhaji Mohammed Magaji ya shaidawa BBC cewa rashin tsaron da aka fama da shi a yanzu ya haifar da matsaloli na bangaren samar da abinci.

Ya ce yawancin jahohin da ake noma kayan abinci na fama da matsalolin tsaro don haka dole ne gwamnatin tarayya ta tashi tsaye a cewar sa.