Shekarau ya zama ministan Ilimi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ibrahim Shekarau ya canza sheka daga APC zuwa PDP

Shugaban Nigeria, Goodluck Ebele Jonathan ya rantsar da sabobbin ministoci hudu a fadar sa da ke Abuja babban birnin kasar.

A cikin ministocin wadanda Majalisar Dattijai ta tattance a makon da ya gabata, an nada tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau a matsayin ministan Ilimi.

Sai Stephen Oru, minista a ma'aikatar kula da harkokin Niger Delta da Abdul Bulama, minista a ma'aikatar kimiya da fasaha sai kuma Clement Adebayo Adeyeye, karamin ministan a ma'aikatar ayyuka.

Shugaba Jonathan kuma ya maida Bashir Yuguda a matsayin ministan tsare-tsare na kasa kuma karamin minista a ma'aikatar kudi.

Mr Jonathan ya bukaci sabbin ministocin su yi amfani da gogewarsu wajen ciyar da kasar gaba.

Karin bayani