Gwaji da dabbobi ya dan karu a Birtaniya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana amfani da beraye a dakunan binciken kimiyya

An dan samu karuwar yin amfani da dabbobi wajen yin gwaje gwajen kimiyya a Birtaniya duk kuwa da alkawarin da gwamnati ta dauka na rage amfani da dabbobin.

Alkaluma sun nuna cewa hanyoyin da aka bi wajen yin gwaje gwaje sama da miliyan 4, an yi sune tare da amfani da dabbobi.

Kungiyoyin dake kare hakkin dabbobi sun ce gwamnati ta saba alkawarin ta na rage yawan wadannan gwaje gwaje ta hanyar amfani da dabbobi

Ana amfani da dabbobi kamar bera da kifi da gafiya da tsintsaye da karnuka da dawaki da shanu da tumaki wajen yin gwaje gwaje

Image caption Kungiyoyin kare dabbobi sun ce gwamnati ta saba alkawarin rage binciken kimiyya da dabbobi

A shekarar 2010, gwamnatin hadaka a Birtaniya ta dau alkawarin inganta sha'anin kula da jin dadin dabbobi.

Sun bayyana cewa: "Zamu kawo karshen gwajin kayayyakin cikin gida akan dabbobi kuma zamu yi aiki domin rage amfani da dabbobi wajen yin bincike na kimiyya"

Wasu kungiyoyin kare hakkin dabbobi dai sun bayyana cewa miliyoyin dabbobi na cigaba da dandana kudarsu da kuma mutuwa a dakunan gwaje gwaje na kimiyya

Sai dai Wendy Jarrett, babbar jami'a a kungiyar "Understanding Animal Research", dake aiki domin kara fahimtar da jama'a a kan binciken kimiyya ta hanyar amfani da dabbobi, ta ce ba daidai bane ace yawan dabbobin da ake amfani da su wajen gwaje gwaje sun karu.

Beraye dai sune kashi uku bisa hudu na dabbobin da ake amfani da su a binciken kimiyya