Za a rusa kasuwar Terminus ta Jos

Hakkin mallakar hoto plateau state govt
Image caption 'Yan kasuwa a Kasuwar Terminus sun bayyana damuwa game da matakin rushe kasuwar

Gwamnatin jihar Filato dake tsakiyar Najeriya ta bayyana cewa zata rusa kasuwar nan ta yankin Terminus dake Jos babban birnin jihar

A cikin watan Mayu ne dai aka kai tagwayen hare-haren bama-bamai da suka yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dari da kuma janyo hasarar dimbin dukiya a kasuwar.

Gwamnatin dai ta bayyana cewa zata rusa kasuwar mai daruruwan shaguna, da kuma haramta hada-hada a daukacin yankin saboda abin da ta kira dalilai na tsaro da kuma kiyaye lafiyar jama’a.

To sai dai kuma ‘yan kasuwa da matakin gwamnatin zai shafa, na cewa gwamnatin bata nuna damuwa kan mawuyacin halin da suka shiga sakamakon hasarar da suka tafka a harin bama-baman.

'Yan kasuwar sun kuma yi zargin cewa akwai boyayyiyar manufa da ta sa gwamnatin daukar wannan matakin.