Ba zan bayyana gaban kwamiti ba - Nyako

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan majalisa sun lashi takobin tsige Gwamna Nyako

Gwamnan jihar Adamawa a Nigeria, Murtala Nyako, ya ce ba zai bayyana a gaban kwamitin da ke gudanar da binciken zarge-zargen ake masa na karkatar da akalar wasu makudan kudaden na jihar ba.

Kwamitin wani bangare ne na yunkurin da majalisar dokokin jihar Adamawa ke yi na tsige Gwamna Nyako da mataimakinsa, Bala Ngilari.

A ranar Laraba ne kwamitin da babban alkalin jihar ya kafa, ya gayyaci gwamnan da mataimakinsa su bayyana a gabansa domin kare kansu daga zarge-zargen.

Rahotanni kuma na cewa Gwamna Nyako ya koma Yola, babban birnin jihar bayan da ya shafe lokaci mai tsawo a Abuja a kokarin samun maslaha ga dambarwar shirin tsige shi da mataimakin nasa.

Da dama na kallon cewar, akwai batun siyasa a batun tsige Gwamnan, saboda ya bar jam'iyyar PDP mai mulki ya koma jam'iyyar adawa ta APC.

Karin bayani