Yaran Nigeria na fama karancin abinci

Kananan Yara a Nigeria
Image caption 'Yan Nigeria 8,000 da suka tsallaka kan iyaka zuwa Kamaru tun watan Mayu.

Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana fargaba a kan tsananin rashin abinci mai gina jiki da kananan yaran arewacin Nijeriya da ke gudun hijira a Kamaru.

Hukumar ta ce tana samar da kayayyakin agaji ga 'yan Nijeriya kusan 8,000 da suka tsallaka kan iyaka zuwa Kamaru tun a watan Mayu.

Akasarin mutanen na zaune ne a kauyukan da ke kusa da bakin iyaka, inda sha'anin tsaro ke kara tabarbarewa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce 'yan Nijeriya kimanin dubu 650 ne rikicin Boko Haram ya raba da matsugunnansu a jihohi uku na arewa maso gabashin kasar da suka fi fama da rikicin Boko Haram.