Boko Haram: 'Yan Nigeria na fama da yunwa

Hakkin mallakar hoto NEMA
Image caption Wasu daga cikin wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu

Hukumar abinci ta duniya WFP ta bayyana damuwa matuka dangane da matsalar tamowa da kananan yara 'yan gudun hijirar Nigeria da suka tsallaka cikin Kamaru ke fama da ita.

Hukumar ta WFP, tana samar da kayan abinci ga 'yan Nigeria kusan dubu 80 da suka nemi mafaka a Kamaru tun cikin watan Mayu saboda hare-haren 'yan Boko Haram.

Hukumar ta ce 'yan gudun hijirar na Nigeria suna zaune a kauyukan da ke kan iyaka da Kamaru inda ake zaman dar-dar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce 'yan Nigeria kusan dubu 650 ne suka bar muhallinsu a jihohi uku da matsalar ta Boko Haram ta fi shafa.

'Yan Boko Haram sun kashe dubban mutane a Nigeria, sannan fiye da watanni uku kenan da suka sace dalibai 'yan mata kusan 300, wadanda har yanzu ba a kubutar da su ba.