'Kudaden man Nigeria ba su bace ba'

Majalisar dokokin Nigeria Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption Kwamitin majalisar ya binciki zargin wawure kudade a kamfanin mai na kasar

Kwamitin da majalisar dattawan Nijeriya ya kafa kan zargin wawure wasu kudaden man fetur ya ce babu kudade da suka bace.

Hakan na kunshe ne cikin rahoton kwamitin, wanda ya binciki zargin da tsohon Gwamnan babban bankin Nijeriya, Malam Sanusi Lamido Sanusi ya yi a baya cewa wasu kudade kimanin dala miliyan 49 sun bace.

Sai dai shugaban kwamitin Sanata Ahmed Makarfi ya shaida wa BBC cewa akwai kimanin dala miliyan 262 da hukumomi suka ce an yi amfani da su amma kwamitin bai ga hanyoyin da aka bi wajen kashe kudaden ba.

Furuci da Malam Sanusi Lamido ya yia wancan lokacin ya janyo rikici tsakanin sa da shugaban kasar wanda ya bukace shi da ya yi murabus daga kan mukaminsa.

Daga bisani shugaba Jonathan ya dakatar da tsohon gwamnan babban bankin daga mukaminsa bisa zargin sa da sakaci da kudade da kuma rashin da'a, zargin da Mallam Sanusi Lamido ya musanta.