Pablo ya ce sun kara kaimi saboda Brazil

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Pablo Zabaleta ya nuna kwazon 'yan Argentina

Dan bayan Kasar Argentina Pablo Zabaleta ya yi amannar cewa masu goyon bayan Brazil da suka nuna adawa garesu ya sa su azama a gasar cin kofin duniya.

Kasashen biyu dai sun jima suna kasancewa masu adawa da juna a fagen wasannin kwallon kafa.

Dan bayan wanda yake bugawa Manchester City ya ce abune mai kyau garesu da suke wasa a kasar Brazil.

Acewarsa sunji dadi musamman ma saboda masoya kwallon kafar Brazil da suka nuna adawa gare su a wannan gasar cin Kofin kwallon kafar na duniya.

Karin bayani