Shugabannin BRICS za su yi taro a Brazil

Hakkin mallakar hoto brics
Image caption Kasashen BRICS na korafin cewa ba a damawa da su yadda ya kamata a fagen siyasar duniya

Bayan da suka kammala kallon wasan karshe na Gasar Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya, shugabannin kasashen Brazil, da Rasha, da India, da China, da Afirka ta Kudu za su nufi Fortaleza, inda za a gudanar da taron koli na shida na kasashen BRICS.

Ranar Litinin ministocin kudi da shugabannin manyan bankunan kasashen za su gana, sannan ranar Talata ake sa ran bayar da sanarwar kafa wata sabuwar cibiyar kudi wacce za ta kalubalanci Bankin Duniya da ire-irensa.

A shekara ta 2001 ne dai wani masanin tattalin arziki ya kirkiri kalmar BRICS bayan da ya dunkule kasashen wuri guda wadanda ya ce su ne za su fi kowacce kasa karfin tattalin arziki nan gaba.

Sai dai masu suka sun ce babu abin da ya hada kasashen; amma dai abu guda da ko waccensu ke korafi a kansa shi ne cewa ba a ba ta matsayin da ya dace da ita a fagen siyasar duniya, musamman ma ganin cewa su ne ke da kashi arba'in cikin dari na al'ummar duniyar.

Don haka ne manufar sanarwar da ake sa ran za su bayar a wannan makon ita ce gyara wannan matsala.

Cibiyar kudin da za a kafa, wacce za a kira Sabon Bankin Raya Kasashe, za ta rika samar da kudi ne don ayyukan samar da ababen more rayuwa a kasashe masu tasowa.

Ana kuma rade-radin cewa za a samar da wani asusu da zai rika taimakawa kasashen na BRICS idan suka ci karo da matsalar tattalin arziki.

Ko da yake bankin ba zai yi tasirin Bankin Duniya nan take ba, yunkurin kafa shi kadai ma abu ne mai muhimmanci sosai, don kuwa shi ne cibiya ta farko da kasashen na BRICS za su kafa a hukuamnce.

Karin bayani