Chibok: Malala ta gana da Jonathan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Jonathan ya ce zai gana da iyayen 'yan matan

Yarinyar nan 'yar Pakistan, Malala Yousafzai, ta gana da Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan game da 'yan matan Chibok da aka sace.

A ranar Litinin ne 'yan matan Chibok fiye da 200 suka kwashe watanni uku cur a hannun kungiyar Boko Haram da ta sace su.

Haka kuma Malala za ta gabatar da jawabinta na Ranar Malala, wanda zai mayar da hankali ga sace 'yan matan da aka sace a makarantarsu da ke garin Chibok a Jihar Borno.

Tun ranar Asabar ne Malala da mahaifinta suka isa Abuja, babban birnin Nigeria, kuma a ranar Lahadi ta gana da 'yan kungiyar #BringBackOurGirls, masu fafutukar ganin gwamnati ta kwato 'yan matan Chibok.

Haka zalika, Malala ta gana da iyayen wadansu daga cikin 'yan mata na Chibok da ma wasu daga cikin 'yan matan da suka tsere.

Wadansu daga cikin iyayen 'yan matan sun fashe da kuka lokacin da suka yi ido hudu da Malala, sun kuma bayyana cewa ganinta ya kara musu kwarin gwiwar cewa 'ya'yan nasu za su dawo.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shekaru biyu da suka wuce ne wani dan Taliban ya harbi Malala a ka, amma likitoci a Burtaniya suka cece ta

Karin bayani