Mu muka kai harin Abuja da Lagos —Shekau

Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Abubakar Shekau

Jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya amsa cewa kungiyarsu ce ta tayar da bam a wani dappon mai da ke Lagos, da ma wasu hare-hare da aka kai a Kano da Jos da kuma Abuja.

A yau ne dai aka fitar da wannan hoton video.

A bayanin da ya yi dai ya kai a kalla tsawon minti goma sha daya, ya yi ikirarin cewa su ne suka kai hare-haren bom a wasu sassan Najeriya a dan tsakanin nan, a Kano da Kano, da Abuja, da kuma Lagos.

kazalika cikin jawabin nasa ya yi mubaya'a ga wasu malamai da kungiyar ke ganin girma da darajarsu, yayin da kuma ya soki lamarin wasu.

Ya fito ne sanye da kayan damara na soja da bindigar AK 47 a wuyansa, kafarsa kuma ya sanya takalmin ruwa, a baya da kuma gefensa kuma wasu tankokin yaki ne da wasu zarata rike da wasu manyan bindigogi masu jigida da tutoci.