Faransa ta kaddamar da farmaki a Sahel

Jiragen yakin Faransa Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jiragen yakin Faransa

Faransa ta kaddamar da wani sabon farmaki na dogon lokaci a yankin Sahel da kuma a arewacin Afirka, domin dakile barazanar kungiyoyi masu jihadi.

A karkashin shirin, Faransar za ta jibge sojoji dubu uku a yankin da ya kama daga Mauritania a yamma, zuwa Chadi a gabas.

Hakan na faruwa a daidai lokacin da kasar ta Faransa ta kitse farmakin sojan da ta kaddamar watanni sha takwas da suka gabata, a kan masu kishin Islama a Mali.

'Yan tawayen Abnizinawa a baya sun yi kokarin ballewa daga kasar Mali domin kafa daular musulunci.

Lamarin ya janyo hasarar rayuka da dukiyoyi.

Karin bayani