An sake kara kudin man fetur a Ghana

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba John Dramani Mahama na shan suka kan wannan matakin

A karo na uku a cikin wannan shekarar, gwamnatin Ghana ta sake kara farashin albarkatun man fetur da dangoginsa.

An kara farashin man fetur da kashi ashirin da uku cikin dari, sannan kuma an kara farashin kalanzir da kuma dizil.

Hakan ya sa kungiyoyi masu motocin sufuri su ma suka kara kudaden shiga motocin da kashi sha biyar bisa dari.

Tun daga karshen makon sabon kudaden shiga motocin sufuri ya soma aiki.

An kara kudin shiga motoci ne bayan tattaunawa tsakanin ma'aikatar sufuri da kungiyar masu motocin sufuri.

Al'ummar Ghana sun koka da wannan karin, inda suka ce hakan zai kara musu kuncin da suke fuskanta.