An kashe mutane 172 a Gaza

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hare-haren Isra'ila sun haddasa mutuwar daruruwan mutane da asarar dukiya mai yawa a Gaza

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta ce mutane 172 aka kashe tun bayan da Isra'ila ta fara kai hare-hare ta sama a kan zirin Gaza.

Ma'aikatar ta kuma bayar da alkaluman mutanen da suka jikkata, wadanda suka haura dubu daya da dari biyu.

Babu wani dan kasar Isra'ila da ya mutu sakamakon harba rokokin da Hamas ke yi daga zirin, amma an kakkabo makamai masu linzami guda biyu da aka harba kan Tel Aviv.

Isra'la ta ci gaba da kai hare-hare a arewacin zirin na Gaza bayan da ta gargadi mazauna yankin su fice daga gidajensu.

Rundunar sojin Isra'ilar dai ta ce tana kai harin ne a kan wuraren da Hamas ke harba makaman roka.

Dubban Falasdinawa ne suka bar gidajensu a yankin arewacin Gaza bayan gargadin an Isra'ila.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane 17,000 sun nemi mafaka a cibiyoyinta yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare.

Karin bayani