Sudan ta hana gina sabbin coci a kasar

Hakkin mallakar hoto AP

Majalisar coci coci a Sudan ta soki lamirin hukumomin kasar dangane da haramta gina sabbin coci coci a fadin kasar.

Babban sakataren majalisar Kori El Ramli yace ya yi mamakin sanarwar da aka fitar a ranar Asabar cewa gwamnati ba za ta sake bada da izinin gina wani choci ba.

Sai dai ministan mai kula da bada shawara da tallafin addinin Shalil Abdullah yace yawan choci chochin da ake da su a Sudan sun isa su wadatar da Kiristoci a fadin kasar.

Karin bayani