Tsare bayani: korafi ya karu a Burtaniya

Image caption A cewar ofishin, mutnae na bukatar mai sa ido a kan bayanansu

Kwamishinan yada labarai na Burtaniya ya yi kira a kara kudin da ake baiwa ofishinsa mai sa ido a kan al'amuran musayar bayanai saboda yawan batutuwan da yake dubawa ya yi tashin gwauron zabi.

Kwamishinan, Christopher Graham, ya ce hukumar na bukatar "karin iko" ne gabanin fitar da rahoton shekara-shekara na Ofishin Kwamishinan Yada Labarai.

A shekara guda da ta gabata, ofishin ya ladabtar da kamfanonin da aka samu da laifin keta dokar tsare sirrin bayanai da tarar da ta kai fam miliyan daya da dubu dari tara da saba'in.

Rahoton ya zayyana yadda yawan keta dokar tsare sirrin bayanai a matakin kananan hukumomi ya karu, musamman ma "bankada bayanan daidaikun mutane bisa kuskure".

A daya daga cikin misalan da rahoton ya bayar, wani jami'i ya amsa laifin bayyana adireshin wani da aka ci zarafinsa ga wanda ya ci zarafin. An dai ci tarar jami'in fam 150.

Ofishin Kwamishinan Yada Labaran ya ce ya warware takaddama a kan koke-koken da suka shafi tsare sirrin bayanan mutane har guda 15,492.

Hakkin mallakar hoto thinkstock
Image caption Ofishin ya ce da dama daga cikin korafe-korafen a kan kiraye-kirayen waya ne na ba-gaira-ba-dalili

Hakan na nuni da cewa korafe-korafen sun karu da kashi goma cikin dari idan aka kwatanta da watanni goma biyu da suka gabata.

Yawan kiraye-kirayen waya ga ofishin kuma ya karo da kashi goma sha biyar cikin dari.

An kuma yanke hukunci a kan mutane 12 da Ofishin ya gurafanar a gaban kuliya saboda bayyana bayanan daidaikun mutane ko zakulo bayanan ba bisa ka'ida ba.

Yayin gabatar da rahoton ranar Talata, ana sa ran Mista Graham zai ce: "(Idan aka dubi) Facebook, da bayanan inshorar lafiya, da Google, a zahiri take cewa yadda kamfanoni da hukumomi ke amfani da bayanai na kara sarkakewa. Don haka mutane na bukatar sanin cewa akwai wanda ke sa ido a kan bayanansu".