An tsige Gwamna Nyako na Adamawa

Image caption Gwamna Murtala Nyako na APC

Rahotanni daga jihar Adamawan Nigeria na cewa 'yan majalisar dokokin jihar sun tsige gwamnan jihar Murtala Nyako daga mukaminsa.

Wani babban jami'in gwamnatin Adamawa, ya tabbatarwa BBC cewar, dazu nan 'yan majalisar suka tsige Gwamna Nyako.

Tun a cikin watan da ya gabata ne 'yan majalisar suka fara yinkurin tsige gwamnan bisa abinda suka ce saba ka'idar aiki da almubazzaranci da dukiyar al'umma.

Kwamitin da babban mai shari'a a jihar Adamawa ya kafa domin binciken gwamna Nyako a ranar Litinin ya mika rahotonsa.

Kwamitin ya gayyaci Murtala Nyako da mataimakinsa, Bala Ngilari amma dukkansu suka ki bayyana gaban kwamitin domin su kare kansu.

Mutane da dama na ganin cewar tun lokacin da Murtala Nyako ya koma jam'iyyar adawa ta APC daga jam'iyyar PDP mai mulkin kasar, aka soma jita-jitar za a tsige shi.