An rantsar da mukaddashin gwamna a Adamawa

Tshon gwamnan Adamawa Murtala Nyako
Image caption Tshon gwamnan Adamawa Murtala Nyako

An rantsar da kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Nigeria Alhaji Ahmad Umar Fintiri a matsayin mukaddashin gwamna, bayan da majalisar dokokin ta tsige gwamnan jihar Murtala Nyako dazu da rana.

Mukaddashin babban alkalin jihar da ake cece-kuce kan karewar wa'adin aikinsa ne ya rantsar Alhaji Ahmadu Fintiri, kuma tuni sabon mukaddashin gwamnan ya yi wa al'umar jihar jawabi ta kafofin watsa labarai.

Mukaddashin gwamnan ya yi kiran kwantar da hankula tare da alkawarin biyan albashin ma'aikatan gwamnati, wanda aka shiga wata na biyu ba a biya ba, sabo da matakin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya EFCC ta dauka na rufe asusun gwamnatin jihar dangane da dambarwar tsige gwamnan.

Majalisar jihar ta Adamawa dai ta tsige gwamna Murtala Nyako ne bisa zargin almubazzaranci da dukiyar jihar, amma yana cewa bata bi ka'ida ba kuma zai ci gaba da kalubantar tsarin da ta bi a kotu

Karin bayani