'Yan Boko Haram sun kashe mutane 2,000

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau ya ce zai sako 'yan Chibok idan aka saki 'yan Boko Haram

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta ce kungiyar Boko Haram ta kashe fararen hula 2053 a Nigeria a wannan shekarar.

Human Rights Watch ta ce mutanen sun halaka ne a hare-hare daban-daban kusan 95 a garuruwa sama da 70 a shiyyar arewa maso-gabashin Nigeria.

Daraktan hukumar na Yammacin Afrika, Corinne Dufka ya ce "Rashin imanin da ake nuna wa a hare-haren da ake kai wa fararen hula laifi ne a kan bil adama, kuma za a hukunta wadanda suka aikata shi."

Shugaban kasar, Dr Goodluck Jonathan na fuskantar matsin-lamba cewa ya gaggauta kawo karshen rikicin Boko Haram tare da kubuto da 'yan matan sakandaren Chibok da aka sace watanni uku da suka wuce.