Chibok: Iyaye sun gwale shugaba Jonathan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Watanni uku kenan da sace 'yan matan na Chibok

Wasu daga cikin iyayen yaran nan 'yan makarantar Chibok da aka sace a jihar Borno, sun ce ba za su gana da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ba kamar yadda aka shirya yi.

A ranar Litinin ne fadar shugaba Jonathan ta fitar da sanarwa cewa, shugaban kasar zai gana da iyaye 12 da wasu daga cikin 'yan matan da suka tsere biyar a ranar Talata.

Gayyatar ta zo ne bayan yarinyar nan 'yar Pakistan Malala Yousafzai ta gana da shugaba Jonathan, inda ta nemi ya gana da iyayen.

Image caption Malala ta gana da wasu daga cikin shugabannin kungiyar Bring back our girls

Wasu bayanai na nuna cewa iyayen sun ce yawansu bai kai yadda za su wakilci dukkan iyayen 'yan mata fiye da 200 da aka sacen ba.

Sai dai a wata sanarwar da fadar shugaban ta fitar, gwamnati ta ce masu fafutukar ceto 'yan matan Chibok na Bring back our girls ne suka sanya siyasa cikin lamarin.

"Hakan abin kunya ne a gare su" In ji sanarwar, inda gwamnatin ta jaddada aniyarta na ceto 'yan matan na Chibok.