Ana shirin tsagaita wuta a Gaza

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Isra'ila ta ce ta kai hari a kan wurare kusan 1,000 a zirin Gaza

Isra'ila da Hamas sun ce suna duba wani shiri da Masar ta gabatar na tsagaita wuta a zirin Gaza.

Ma'aikatar harkokin wajen Masar ce dai ta gabatar da shirin ana gab da fara wani taron gaggawa na Kungiyar Kasashen Larabawa a birnin Alkahira.

Shirin tsagaita wutar ya bukaci Isra'ila da Hamas su dakatar da kai hare-hare daga safiyar ranar Talata.

Ministan harkokin wajen Masar, Sameh Shukry, ya ce wannan shiri na Masar ya ta'allaka ne a kan dakatar da kai hare-hare nan take, da sake bude hanyoyin shiga Gaza, da kuma aiwatar da shirin tsagaita wutar bayan bangarorin sun amince su daina yi wa juna kallon hadirin kaji.

Nan gaba kadan ne majalisar tsaro ta Isra'ila za ta tattauna a kan shirin.

Ministan tsaron kasar, Moshe Yaalon, ya ce zuwa yanzu Isra'ilar ta lalata abubuwa kusan 1,500 wadanda suka hada da makaman roka, da taskokin adana makamai, da masana'antun makamai, da cibiyoyin ba da umarni, da kuma gidajen kwamandojin Hamas kusan 150, da ofisoshi, da cibiyoyin gwamnati, da cibiyoyin kudi da kadarorinsu.

Jagoran Hamas, Isma'il Haniyah ya ce a shirye suke su tsagaita wuta, sai dai kuma babu tabbas a kan ko kungiyar za ta amince da sharuddan da ke kunshe a cikin shirin da Masar ta gabatar.

Falsdinawa sun ce fiye da mutane 180 aka kashe a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa.

Karin bayani