An ceto yara da ake lalata da su a Mexico

Attoni Janar na Mexico Hakkin mallakar hoto Milenio
Image caption Attoni Janar na Mexico

Hukumomi a kasar Mexico sun ce an kubutar da yara kimanin dari biyar daga wani gidan Marayu bayan an yi zargin cewa ana lalata da su tare kuma da tilasta musu bara a kan tituna.

An kame mai gidan marayun "house of the big Family" dake jihar Micoacan da wasu ma'aikata 8. Masu aiko mana labarai sun ce wannan yana daya daga cikin al'amurra mafi muuni da aka samu a kasar na cin zarafin yara tun shekaru da daama da suka wuce.

An ce an tsare yaran ne ana lalata da su da kuma gallaza musu tare da ba su abincin da bai kamata a ciyar da dan adam irinsa ba.

Wakilin BBC ya ce yara fiye da 450 ne da kuma manya aka gano a wannan cibiya ta kula da marayu karkashin wani yanayi maras kyau.

Karin bayani