Pakistan ta ba da taimako ga Nijer

Mutanen da Fari ya shafa Nijer
Image caption Mutanen da Fari ya shafa Nijer

A jumhuriyar Nijar hukumomin Pakistan sun ce sun tallafa ma kasar da kudade dollar Amurka kusan dubu dari a matsayin gudumuwarsu.

Kakakin ministan harkokin wajen kasar ta Pakistan ne ya tabbatar da haka da nufin tallafa ma jama'ar kasar da fari ya shafa a bara.

Wannan tallafi dai ya zo ne a daidai lokacinda wasu al'ummomi makiyaya na kasar ta nijar ke kukan dabbobinsu na mutuwa sakamakon rashin abinci.

To amma gwamnatin kasar na cewa tuni ta dauki matakan tallafa musu da dusa da kuma gurya.

Karin bayani