'Jonathan na da hannu a tsige Nyako'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Rabi'u Musa Kwankwaso na daya daga cikin gwamnonin da suka bar PDP zuwa APC

Gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya yi zargin cewa Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne ya cire Murtala Nyako amma ba 'yan majalisa ba.

Gwanan yana maida martani ne bayan da 'yan majalisar dokokin jahar Adamawa suka tsige Murtala Nyako a matsayin gwamna ranar Talata

Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar APC ya zargi shugaban Nijeriya da jam'iyyar PDP da hannu dumu-dumu a tsigewar da aka yi wa Murtala Nyakon.

Gwamnan na Kano ya ce baya ga Murtala Nyako an kuma tasa wasu gwamnonin APC a gaba, wanda ya ce hakan ba karamar illa ba ce ga dimokradiyya.