Fyade: Za a daure maza biyar a Masar

Image caption An yi zanga-zangar adawa da fyade da kuma cin zarafin da ake wa mata a Masar

Wata kotu a Masar ta yanke wa wasu maza biyar hukuncin daurin rai da rai, bisa aikata lalata da wasu mata.

Haka kuma kotun ta yanke hukuncin dauri na tsawon lokaci ga wasu mazan biyu da aka samu da laifin yunkurin yin fyade da kisa da kuma azabtarwa.

A lokacin bikin rantsar da sabon shugaban kasar ta Masar ne Abdul Fattah al-Sisi aka yi lalata da matan.

Masu aiko da rahotanni sun ce hukuncin zai dan rage damuwar da ake nuna wa game da gazawar hukumomi wajen magance matsalar cin zarafin mata.

Karin bayani