Jonathan ya aika takardar gayyata Chibok

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Malala Yousafzai ce ta nemi shugaba Jonathan ya gana da 'yan Chibok din

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya aika wasika ga al'ummar garin Chibok, inda ya bukaci ganin iyayen 'yan matan da aka sace.

Haka kuma ya bukaci ganin 'yan matan da suka samu tserewa daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram.

Shugaba Jonathan na son ganawa da iyayen ne a mako mai zuwa.

A ranar Talata ne wasu iyayen 'yan matan na Chibok suka gwale shugaban kasar, inda suka ki halartar taron da ya kira su.

'Yan matan 'yan makaranta fiye da 200 sun kwashe watanni uku kenan a hannun Boko Haram, kuma gwamnati ba ta gana da iyayen ba a tsawon wannan lokaci.