Holland na da laifi a kisan musulmin Bosnia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Musulmi kusan 8,000 aka kashe a yakin Bosnia

Wata kotu a kasar Holland ta dora wa gwamnatin kasar alhakin mutuwar wasu mutane sama da 300 a Srebrenica lokacin yakin Bosnia da aka yi a shekarar 1990 da 'yan kai.

Mutanen dai sun je gudun-hijira ne a wani sansanin majalisar dinkin duniya, amma daga bisani dakarun rundunar wanzar da zaman lafiyar Netherlands suka mika su ga sojojin Sabiyawa, suka kuma kashe su.

Kotun ta ce da gamsu da wasu hujjoji da suka tabbatar da cewa da an kyale mutanen sun ci gaba da zama a sansanin da ba su mutu ba.

Wata kungiyar kare hakkin bil'adama mai suna Mothers Of Srebrenica ce a shigar da karar gwamnatin,tana zarginta da gazawa wajen kare dubban 'yan uwansu mazaje da ke sansanin majalisar dinkin duniyar ko kusa da shi.

Lauyan Kungiyar ya ce hukuncin kotun na da muhimmanci.

Karin bayani