Nyanya:Sudan ta mika wa Nigeria Sadiq Agwuce

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police
Image caption Aminu Sadiq Ogwuche shi ne ya kitsa harin kafin ya arce Sudan

An tasa keyar mutumin da ake zargi da hannu a harin bam na Nyanya a Abuja daga Sudan zuwa Nigeria, bayan da 'yan sandan kasa da kasa suka mika shi ga hukumomi a Nigeria.

Gwamnatin Nigeria ta tabbatar da cewa an mika mata Aminu Sadik Ugwuche wanda ake zargin hannu a harin bama din da ya yi sanadiya mutuwar mutane sama da 75.

A ranar 14 ga watan Afrilu ne aka kai hari a tashar motoci da ke Nyanya inda mutane da dama suka ji raunuka.

A cikin watan Mayu aka damke Aminu Sadiq Ogwuche a Khartoum bayan da 'yan sandan kasa da kasa suka bada sammacin kama shi.

Dubban mutane aka kashe sakamakon rikicin Boko Haram, inda a bana kawai aka hallaka mutane fiye da 2,000.