APC za ta kalubalanci tsige Nyako

Image caption Ana zargin PDP da hannu a tsige Murtala Nyako

Jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria ta ce za ta shigar da kara a kotu domin ta kalubalanci tsige gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako da 'yan Majalisar Dokokin jihar suka yi.

Jam'iyyar kuma ta zargi Shugaban Nigeria da hannu a tsige gwamnan Adamawa da kuma kokarin shirya makarkashiyar tsige gwamnan jihar Nasarawa, Umaru Al Makura.

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Cif John Odigie Oyegun shi ne ya yi zargin a taron manema labarai a Abuja, inda kuma ya yi zargin cewar gwamnati ta baiwa 'yan majalisar dokokin jihar Adamawa kudi kafin su tsige Gwamna Nyako.

A ranar Litinin ne 'yan Majalisar Dokokin jihar Adamawa suka tsige gwamna Nyako sannan aka rantsar da shugaban majalisar dokokin jihar Amadu Umaru Fintiri a matsayin mukaddashin gwamna.

Kawo yanzu gwamnatin Nigeria ba ta maida martani ba game da wannan zargin da 'yan APC din suka yi.

Karin bayani